Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 da jiragen ruwa guda shida domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.
- Tinubu ya bai wa jihohi N108bn domin magance matsalar ambaliyar ruwa
- Sarki Charles ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Buckingham
A cewar sanarwar, Gwamna Fintiri da ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar ya miƙa tallafin ga Gwamna Babagana Zulum, inda ya jaddada buƙatar haɗin kai domin rage raɗaɗin al’ummar da abin ya shafa.
Da yake alhini kan asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ta haddasa, Gwamna Fintiri ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin shawo kan lamarin.
A ziyarar da ya kai, Gwamna Fintiri, tare da takwaransa Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, sun shiga wani jirgin ruwa tare da Gwamna Zulum domin gane wa idanunsu irin asarar da aka yi tare da jajanta wa waɗanda ambaliyar ta tsugunar a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.
Tawagar Jihar Adamawa da suka haɗa da Sakataren Gwamnatin jihar, Awwal Tukur, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, da abokan arziki, sun nuna aniyarsu ta tallafa wa jihohin da ke maƙwabtaka da su a lokutan faruwar irin haka.