✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna El-Rufai ya sake lashen zaben Gwamnan Kaduna – INEC

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya sake lashe zaben Gwamnan jihar a karo na biyu kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar.…

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya sake lashe zaben Gwamnan jihar a karo na biyu kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar.

Jami’in hukumar zaben jihar Farfesa Muhammed Yahuza Bello ya sanar da cewa, Gwamnan Kaduna kuma dan takarar Gwamnan jihar a jam’iyyar APC ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’u 1,045,427 yayin da abokin takararsa na jam’iyyar PDP Alhaji Isah Ashiru ya samu kuri’u 814,168.