✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna El-Rufa’i da rikicin Kaduna

Ko da ba a yi rikicin kasuwar magani ba a Karamar Kajuru ta  Jihar Kaduna ba, duk mai hankali ya san jihar kamar bisa nakiya…

Ko da ba a yi rikicin kasuwar magani ba a Karamar Kajuru ta  Jihar Kaduna ba, duk mai hankali ya san jihar kamar bisa nakiya take tangal-tangal; kai ba ma Kaduna ba, baki dayan kasar nan na bisa nakiya ne.

A Jihar Kaduna, tun lokacin da Nasir Ahmed El-Rufa’i ya zama Gwamnan Jihar Kaduna, babu wani yunkuri na kirki, na a-zo- a- gani da ya yi ko yake yi domin  dakile yiwuyar aukuwar rikicin addini, siyasa da kabilanci a Jihar Kaduna, wadda ke da mummunan tarihin ta da fitintinun rashin hankali da dabbanci da sunan kare addini, jinsi, kabila ko al’ada. Maimakon haka ma, sai gwamna El-Rufa’i ya koma rikici da ’yan siyasa; ’yan siyasar ma, na jam’iyyarsa ta APC ba ma ta adawa ba.

Duk wanda ya kalli fasalin rikicin El-Rufa’i da su Hakim Baba-Ahmed, Shehu Sani, Hunkuyi da sauran su, ya san rikici ne da ya samo asali sakamakon karancin hikima da dabara ta mulki daga gwamna Nasir El-Rufa’i; domin gwamna shi ne uba a jiha, kuma shi ne shugaban kowa. Shugabanci abu ne da ake dasawa bisa wasu ka’idoji da dokoki, kuma salo salo ne. MIsali, akwai salon shugabanci na kama-karya,wanda shugaba bai damu da ya yi amfani da ra’ayin mutane ba; kuma hanyar sadarwa guda daya ce; wato daga sama zuwa kasa.

A salon irin wannan shugabanci, ra’ayin shugaba shi ne, ra’ayi, ra’ayin mukarrabansa da sauran talakawa duk aikin banza ne. Dole duk abin da shugaba ya ce dole a bi shi ko ana so, ko a ba a so.

A irin wannan shugabanci ne za ka ji shugaba na fadin dole a bi; dole a yi, ko an ki ko an so, idan mutum bai so, to ya hau Dutsen kufena ya fado da ka.

Matsaloli irin wannan salon shugabanci yawa gare shi: Na farko, akasari shugaban zai  samu yadda yake so a lokacin, to amma akwai bi baya; domin duk lokacin da mabiyan suka samu dama to za su iya yin zagon kasa; abin da zai rusa abubuwa da dama. Da ma tilasta masu aka yi. Kuma duk abin da mabiya za su yi, tun da ba a tuntube su ba; kuma ba a karbi shawarwarinsu ba; to za su yi ne ba tare da sadaukarwa ba sai don tsoron za a hukunta su; domin suna kallon aikin a matsayin na shugaban ne kawai,ba nasu ba.

Akwai salon shugabanci mai martaba tsarin dimokuradiyya; karbar ra’ayin mukarrabai da sauran al’umma ko da shugaban bai yarda da sahihancin ra’ayin ba. A irin salon wannan shugabanci tun daga kalaman za ka fahimci akwai saussauci,kuma akwai mutuntawa.Ana sauraron hatta ra’ayin ’yan adawa.

Masana kimiyyar siyasa, sun nuna wannan shi ne salon shugabanci mafi inganci, wanda ya fi haifar da da mai ido. Akwai salo-salo da dama ciki har da  mafi rauni wanda shugaba kan mika ragamar shugabanci ga mabiyansa su yi abin da suka ga dama.

Salon shugabancin Gwamnan Kaduna, salo ne na kama-karya wato wanda da turanci ake kira Autocratic Leadership Style. Domin kama daga rushe-rushen gidajen talakawa da sunan tsara gari; ba tare da biyan su cikakkiyar diyya ba zuwa ga batun shirya wa malaman firamaren jarabawa mai cike da cece-ku-ce da batun dole a kyale ya ciwo wa jihar bashin Bankin Duniya, zuwa batun korar hakimai da masu rike da sarautu da sauran su, duk matakai ne, da shi El-Rufa’i yake so, kuma ya tilasta su bisa jama’a ko suna so, ko ba su so, kuma ya yi watsi da duk wasu kiraye-kiraye na masana da dattawa da sauran su.

Mu fahimci cewa duk kyawun manufa, in dai akwai rashin adalci ga wasu mutane komai karancin su, to da wuya ta yi wani tasirin a-zo- a- gani. Domin daya daga cikin shugabannin daular Usmaniyya wato Muhammadu Bello, na cewa mulki na dorewa ne kawai in akwai adalci ko da wanda ke mulkin kafiri ne, kuma ko da Musulmi ke mulkin, in dai akwai rashin adalci komai kankantarsa, to za a ga abin da ba a so.

Mutumin da ya yi wannan kalamin yana cikin wanda suka hanbarar da daulolin sarakunan Hausawa a farkon karni na 19 saboda zaluncinsu.

Saboda haka, gwamnan da tun da ya zo, rikici yake ta yi da mutanen da a kalla, ko ba komai shugabanni ne wadanda ke da mabiya, to da wahala ya kare shugabancinsa yadda yake so. Yanzu ko ba a kara komai ba, an bata tarihin shugabancinsa tun da tun ba a je ko’ina ba an karkashe mutane a banza.

Gwamna El-Rufa’i maimakon ya inganta tsare-tsaren tattaunawa da fahimtar juna da nuna shugabanci nagari wajen nuna tausayi, jinkai da saussauci ga talakawansa, za ka ga abin ba haka yake ba. Maganganunsa masu zafi. Bai damu da aikace-aikacen kungiyoyin farar hula masu assasa fahimtar juna da kauna a tsakanin addinai da kabilu na jihar da ke da su da yawa.

Tun da ya hau gwamna, babu wata muhimmiyar tattaunawa ko taron koli da ya kira da sunan inganta sasanci da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Jihar Kaduna. Siyasarsa kawai yake da rikici da mutane daban-daban. Don haka ya yi sakaci; kuma duk wanda ya yi abin da zuciyarsa ke so, to dole ya ga abin da ba ya so.

Don haka har yanzu lokaci bai kure ba ga Gwamna El-Rufa’i, zai iya karfafa zumunci, tattaunawa da sulhunta al’ummar Jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin manyan manufofin gwamnatin Jihar Kaduna.

A nan, ba ina nufin surutu na fatar baki kawai ba; a’a dole Nasir El-Rufa’i a mulkinsa; a ga yana girmama ’yancin dan Adam, fila-filar dimokuradiyya kamar juriyar adawa, fadin albarkacin baki; sauraron korafe-korafe a kan wasu daga cikin matakan gwamnatinsa; dole El-rufa’i ya koyi hulda kungiyoyin farar hula masu assasa zumunci da fahimtar juna tsakanin addinnai da kabilu, ko ya yarda da irin wadannan kungiyoyi ko bai yarda da su ba.Kazalika dole ne ya sasanta da manyan ‘yan siyasar jiharshi wadanda kan iya amfani da yanayin jihar Kaduna sui ma mulkinsa zagon kasa. El-rufa’i mutum ne da kullum a bakin kafafen yada labarai ke ikirarin hukunta wadanda ke aikata kisan mutane a Kaduna. To a nan dole fa, ya nuna misali; kafin saukarsa mutane su ga mutum nawa aka hukunta bisa ayyukan ta da tarzoma a jihar. Kuma dole El-Rufa’i ya zakulo mutanen da ke daukar nauyin kashe-kashen, a hukunta su, maimakon hukunta ’yan barandarsu. Domin ga dukkan alamu, rikicin Kaduna da akwai wasu mutane da ke shirya shi, su kuma tsara shi, sannan su aiwatar da shi,don sun san babu abin da za a yi masu.Dole ya El-Rufa’i ya dakile kungiyoyin banga da ke birjik a jihar Kaduna ta hanyar samar da ayyukan yi da ba da shugabanci nagari.

Sannan ya ku mutanen Jihar Kaduna yakamata ku daina kashe junanku , ku daina jawo wa kanku fitina da masifa, maimakon haka, kamata ya yi ku hada kawunanku, ku yaki azzaluman ’yan siyasa da shugabanni masu talauta ku da dawwamar da ku cikin kaskanci na yunwa da rashi.

 

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa  08165270879