Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya taya al’ummar musulmi da sauran al’ummar jihar murnar bikin karamar Sallah da kuma kawo karshen azumin watan Ramadan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labaransa da Hulda da Manema Labarai, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu.
- Yadda hidimar gida ba ta hana mata sana’ar dinkin hannu a Zariya
- Dalilin da aka mayar wa Juventus makinta 15 da aka zaftare
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya kuma taya al’ummar musulmin da suka samu damar sauke farali na Umrah murna a kasar Saudiyya tare da yi musu fatan dawowa Najeriya lafiya.
Ya kuma roki Allah SWT da ya sakawa kowa da kowa da suka yi azumin Ramadan da aljannatul Firdausi Ya kuma gafarta musu kurakuransu.
Gwamnan ya bukaci al’umma da su yi addu’ar Allah Ya kara wa Jihar Yobe da ma Najeriya baki daya zaman lafiya mai dorewa.
Buni ya ce azumin watan Ramadan ya koyar da hakuri, ibada, kamun kai, gaskiya, tawali’u, kyautatawa, gafara da sauran kyawawan dabi’un na musulunci wadanda ya kamata a kiyaye su bayan azumi.
Ya tunatar da musulmi mawadata da su bayar da zakka ga mabukata kamar yadda addini ya wajabta
“Bayar da ma’auni na abinci ga matalauta da mabukata daga cikinmu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, ibada ce da ke karfafa dankon hadin kai da samar da jin dadi da soyayya.
“Mu kuma an tunatar da mu cewa bukukuwan Sallah ma lokaci ne na sadaukarwa da karamci, ya kamata mu ci gaba da baiwa makwabtanmu kyauta don ganin rayuwa ta zama mai ma’ana ga sauran mutane.”
“Ina kara mika godiyata ga Allah Madaukakin Sarki bisa irin zaman lafiya da ake samu a fadin jihar nan, kada mu ce za mu dauki doka a hannu kan kisan gilla da aka yi wa wasu mutane a kusa da Buni Gari a Karamar Hukumar Gujba.
“A cikin bakin ciki ne ma muka samu labarin hadarin mota da ya faru a Damaturu inda wasu suka mutu wasu kuma suka jikkata.
“Allah Ya jikan wadanda suka rasun Ya sa su huta lafiya, kuma ina yi wa wadanda abin ya shafa addu’ar murmurewa cikin gaggawa, inji Gwamna Buni.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu, inda ya bukaci da su kasance masu taka-tsan-tsan wajen dakile illolin miyagun abubuwa.
Gwamna Buni ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’ar mika mulki cikin lumana da nasara a kasar.
Gwamnan ya yi wa kowa fatan alheri da gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.