Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ya yi wa fursunoni 153 afuwa a tsakanin gidajen yarin da ke jihar.
Gwamnan ya ce kowanne daga cikin wadanda aka yi wa afuwar za a ba shi N50,000 a matsayin jarin fara sana’a don taimaka wa rayuwarsu, wanda a jimillace kudin ya kama Naira miliyan N7.6.
Da yake jawabi a wajen bikin yin afuwar a ranar Juma’a, gwamnan ya ce kafin daukar wannan mataki sai da ya yi tuntuba da neman shawara daga Majalisar Zartarwa ta jihar.
Ya ce, “Za mu bai wa kowannensu da aka yi wa ahuwa jarin N50,000 don taimaka musu iya dogaro da kai.
“Mun yi amannar karfafa wa masu karamin karfi na daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma hana aikata manyan laifuka,” in ji shi.
Bala ya ce, sun cika sharuddan da suka dace da suka hada da biyan tarar da ke kan kowane fursunan da afuwar ta shafa.
Ya kara da cewa, al’umma ba za ta ci moriyar wadanda aka yi wa afuwar ba muddin aka bari suka ci gaba da zama a gidan yari tare da gaggan barayi.