✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwajin budurci cin zarafin mata ne —Likita

Wani babban likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas ya ce gwajin budurci da ake yi wa mata a asibiti don tantance ko sun…

Wani babban likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas ya ce gwajin budurci da ake yi wa mata a asibiti don tantance ko sun taba tarayya da maza nau’i ne na cin zarafi kuma ya saba doka.

Likitan ya bayyana cewa hakan ne a Ilorin, yayin taron wayar da kai ga ma’aikatan asibitin sha-ka-tafi da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta shirya a Jihar Kwara.

“Hakan kan jefa mace cikin damuwa da rudarwa da fuskantar wulakanci, domin ba a yi wa maza.

“Sannan mutane sun jahilci mene ne ainihin budurcin, saboda abin da suke gani a matsayin budurci zahirin gaskiya ba shi ba ne,” in ji shi.

Ya ce baya ga dokar Najeriyar, ita kanta WHO din ta haramta hakan, domin dalilan da ke sanya wa a yi hakan tsohon tunani ne.

Ya ce akan gudanar da gwajin ne domin tabbatar da mace ba ta taba saduwa da namiji ba, dalilin aurenta ko duba yiwuwar ba ta aikin gwamnati ko kamfani.

WHO, a cewarsa, ta ce wannan gwajin nuna wariya da kyama ne da cin zarafin matan, don haka akwai bukatar a yi watsi da shi.

Ya kuma ce al’adar wasu ’yan Najeriyar ta idan aka aurar da yarinya a daren farkonta ba a ga jini a zanin gadon ba, ba budurwa ba ce shifcin gizo ne, da cin zarafinsu.