Jami’an Sibil Difens sun cafke wani mutum mai shekaru 47 kan zargi yi wa wata mata fyade a gaban ’yarta mai shekaru biyu.
Kakakin Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Kwara, Ayeni Olasunkanmi, ya ce tun a watan Yunin 2022 hukumar ke farautar sa, amma sai a ranar 5 ga watan Janairu ta cafke shi a garin Makwa na jihar Neja, inda ya buya.
- An kori jami’in DSS daga aiki kan yin barazanar kisa
- Dalilan da za a fuskanci karancin fetur na wata 6 a Najeriya —IPMAN
“Bayan mun kama shi, ya fada mana cewa ya haura gidan matar ce lokacin babu kowa, daga ita sai ’yarta mai shekaru biyu kuma a gaban ’yar ya yi wa uwar fyaden ya kuma sace mata kwamfutoci biyu da wayoyin ta biyu da yayi”, in ji Olasunkanmi.
Ya ce har yanzu dai hukumar na farutar wadanda suka sayi kayan daga hannunsa, sannan ya jan hankalin mutane su rika lura da wadanda suke sayen kaya a hannunsu.
Haka kuma ya ce za su gurfanar da mutumin a gaban kotu, domin ya girbi abin da ya shuka.