An tsare wani Sufeto kuma jami’i tawagar sirri ta musamman a Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nassarawa, bi sa zargin yi wa ’yar dan uwansa da yake riko fyade.
Shugaban Kungiyar Lauyoyi Mata ta Kasa Rabi’atu Addra ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Lafiya da ke jihar ranar Laraba.
Ta ce wani ne ya kai wa kungiyar rahoton lamarin, kuma ba su yi kasa a guiwa ba suka shiga bincike.
Ta bayyana cewa an kama dan sandan tare da jaddada tsayuwar dakarsu don ganin an yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata, don hakan ya zamo izina ga na gaba.
Ta kuma yi kira ga ’yan Sanda da su tabbatar da bincike mai zurfi kan lamarin, domin adalci ga wacce aka zalunta.
“Muna samun labari muka hada kai da Kungiyar Yaki da Cin Zarafin Mata da Kananan Yara da kuma rundunar ’yan sanda domin damko wanda ake zargin,” in ji ta.
“Ita kuma yarinyar mun kai ta asibiti mun biya mata kudin magani, sai dai dan nata mai watanni shida a duniya ya rasu.
“Ma’aikatar Shari’a ta jiha ma ta biya kudin gwajin kwayar halitta domin ci gaba da tattara hujjoji kan lamarin.”
Hajiya Rabi’atu ta ce tuni sun sada yarinyar da ahalinta, wacce mutuwar mahifinta ce tun farko ta sanya ta komawa hannun wanda ake zargin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa DSP Ramhan Nansel bai ce komai ba kan lamarin, kuma ya ki amsa kira da sakon waya.