✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guzirin Ma’aurata Don Ramadan (1)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa,…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. A dalilin kusantowar wata mai alfarma na Ramadan, za mu dakatar da maudu’in da muke bayani a kai na matsalolin mata game da bukatar aure don gabatar da bayani kan tanade-tanade, da shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su yi don tarbar watan Ramadan.Da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

1. Inganta niyya da kudurta alheri: Abu na farko, kuma mafi alfanu, shi ne ma’aurata su daura kyakkyawar niyyar cin ribar wannan muhimmin lokaci don dacewa da dukkan alherin da ke cikinsa. Za su yi haka ne ta hanyar kudurta wa ransu dagewa wajen yin dukkan aiyukan ibada da na kyautatawa don su samu dacewa da rahma da gafarar da Allah ya yi tanadi ga bayinsa da suka aikata kyawawan aiyuka a cikin wannan wata. Haka kuma in ma’aurata suka kudurta wa kansu yin ayyukan alheri cikin wannan wata, wannan zai kara masu taushin zuciya ya kuma bude masu hanyar karuwar imani. Kamar yadda Annabi (SAW) ya sanar mana cewa dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, don haka duk wani aikin da ma’aurata ke son aiwatar da shi cikin Ramadan, to sai su fara da kulla masa kyakkywar niyya tun yanzu. Kuma su tabbatar da niyyar nan cikin zuciyarsu, sannan kullum su yi ta kara jaddada wa kansu wannan niyya.Koda ta hanyar rubatawa a takarda don karantawa kullum har sai wannan niyya ta zama babba kuma sanannen kudiri cikin zuciyarsu.Wannan zai zama garanti gare su na cewa lallai idan Ramadan ya tsaya, to za su samu nasarar aiwatar da dukkan ayyukan alherin da suka yi niyya. Haka kuma ma’aurata suna iya rubuta kudirorin da suke son cimma aiwatar da su cikin Ramadan a takarda, tare ko daban-daban, sai su rika yawan karanta su don jaddada su cikin ma’aikatar hankalinsu. Ga misalan wasu kudirori masu kyau da ya kamata ma’aurata su yi kokarin jaddada su da aiwatar da su cikin Ramadan:
• Yin amfani da watan Ramadan don neman kara kusanci ga Allah (SWT) da kuma kara kusantar juna.
• Yin hakuri da kau da kai ga kura-kuran juna.
• Gyara tare da kara kyautata dangantakar auratayyarsu.
• Hada kai da taimakon juna wajen yin ibada.
• kara wa juna karfin gwiwa wajen dagewa ga yin ayyukan ibada.
• Taimaka wa juna wajen kula da gida, musamman ta fannin hada kayan buda baki da sahur, da kuma kula da tarbiyyar yara.
• Yin kokarin kawar da wata dabi’a maras kyau, wani sabon Allah ko wani laifi da ake yawan aikatawa a cikin gidan, gare su duka ko ko a daya daga cikinsu.
• Yanke kallon fina-finai ko wasannin banza a talabijin a cikin wannan wata gaba daya.
• Daina almubazzaranci, watau wulakanta abubuwan rahmar da Allah ya ni’imta bayinsa da su, kamar abinci, kayan saka wa, ruwa, kayan amfanin gida da kuma lokaci.
• Annabi (SAW) ya yi umarni da a nemi dacewa da lailatul kadari, don haka yana da kyau ma’aurata su sa wannan cikin kudurorinsu na Ramadan.
Da sauran kudirori masu kyau da suka dace da ma’aurata da yanayin rayuwarsu.
2. Gyara zuciya: Duk daya daga cikin ma’aurata, miji ko mata, da ya ji yamutsi ya yi yawa cikin zuciyarsa, to kada ya yarda Ramadan ya riske shi a haka, ya yi kokarin sama wa zuciyarsa natsuwa da aminci ta wadannan hanyoyin:
• Yawan karanta ayoyin kur’ani safe da maraice, ka’in da na’in. Tabbas, duk mai yin haka cikin dan kankanen lokaci zai nemi wannan yamutsi ya rasa kuma ya ji hankalinsa ya kwanta kuma tunaninsa ya daidaita. Kamar yadda Allah (SWT) ya sanar mana cikin littafinsa mai girma, Suratul Ra’ad, Aya ta 28:
“Wadanda suka yi imani, zukatansu su kan natsu da ambaton Allah, to da ambaton Allah ne zukata suke natsuwa.”
Wannan ke tabbatar mana da cewa karatun al kur’ani yana sa zuciya natsuwa da farin cikin da ba su misaltuwa, kuma yana tsabtace hankali, tunani, da shau’ukan cikinta.
• Tuba kyakkyawa: Wannan na samuwa ne lokacin da mutum ya yi tsananin nadamar laifukan da ya sabi Allah da su, ya ji haushin kansa kuma ya ji nauyi da daudar zunubinsa. Sannan ya koma ga Allah ya nemi gafara cikin nadama da kankan da kai ga Allah, sannan da yawan yin istingifari safe, rana da daddare, ka’in da na’in.Ko shakka babu tuba irin wannan yana wanke zuciya daga daudarta kuma yana saukar mata da natsuwa da aminci.
• Sadaka/Kyauta: Yawan kyauta da yin sadaka ga mabukata yana saukar da farin ciki cikin zuciya, wannan wani sirri ne da masana kimiyya ma sun tabbatar da shi.Don haka duk mai fama da yamutsin zuciya sai ya yawaita yin kyauta kafin da kuma cikin watan Ramadan.
• Haka kuma ana gyara zuciya ta hanyar kawatata da ayyuka masu kyau, rayata da yawan tunanin Allah da kyautata zato gare shi da kuma guje wa aikata ayyukan sabon Allah da munana zato ga Allah (SWT), da kuma guje wa munanan tunani da munanan dabi’u.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.