✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gulbi ya ci matashi a Kano

Matashi ya nutse a ruwa ya mutu a Jihar Kano

Matashi Ashfa Ibrahim, dan shekara 14 a Kano, ya rasu bayan nutsewa a ruwa ranar Litinin a kauyen Danzaki cikin Karamar Hukumar Gezawa, Jihar Kano.

Mai magana da yawun Hukumar Kwana-kwana ta jihar, Saminu Abdullahi, ne ya bayyana haka cikin sanarwar da aka raba wa manema labarai ran Talata a Kano.

“Mun garzaya zuwa inda lamarin ya faru bayan kira da muka samu daga wani Ibrahim Abdullahi, ko da jam’ianmu suka isa, sun ceto matashin a galabaice.

“Daga bisani likitoci suka tabbatar da ya riga mu gidan gaskiya a Babbar Asibitin Gezawa,” in ji shi.

Ya ce ana kyautata zaton marigayin ya zame ne ya fada a kududdufin da ya yi ajalinsa.

Ya ce an mika gawar marigayin ga Dagacin kauyen Danzaki, Muhammed Abdulkarim, don yi mata jana’iza.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito an mika batun ga ’yan sanda don zurfafa bincike.

(NAN)