✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwar Batsirai ta hallaka gommai a Madagascar

An rasa rayuwar gomman mutane a sakamakon guguwar da aka yi wa lakabi da Batsirai mai karfin gaske da ta ratsa kasar Madagascar cikin daren…

An rasa rayuwar gomman mutane a sakamakon guguwar da aka yi wa lakabi da Batsirai mai karfin gaske da ta ratsa kasar Madagascar cikin daren Asabar zuwa Lahadi.

Wannan ibtila’i ya tilasta wa mutane kusan 50,000 barin gidajensu tare da fuskantar hadarin ambaliya.

Shugaban Hukumar Kula da Bala’o’i a Madagascar, Paolo Emilio Raholinarivo, cikin wani sako da ya aike wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya tabbatar da mutuwar mutane 6 sannan wasu kusan dubu 48 suka rasa matsugunansu, a matsayin bayanan wucin gadi.

Hukumomin Madagascar sun nuna cewa karfin guguwar ta ragu, sai dai har yanzu akwai fargabar ambaliyar ruwa.

A halin yanzu dai ma’aikatan agajin gaggawa a Madagascar na ci gaba da tantance irin barnar da guguwar Batsirai ta yi, inda bayanai ke cewa ta yi awon gaba da kauyuka da dama.

Guguwar mai karfi wacce ta yi mummunar barna ta afka wa tsibirin ne a karo na biyu cikin mako biyu.

Bayanai sun ce rufin gidaje da dama sun rufta, baya ga gine-gine da suka rushe, ga kuma kakkarfar iska mai tafiyar kilomita 160 cikin sa’a guda.

A wasu wurare ana ma fargabar zaftarewar kasa ta yi gagarumar barna.

Ta’asar da guguwar Batsirai ta yi a garin Mananjary da ke Gabashin kasar ta fi ta ko’ina, inda guguwar ta ratsa a tafiyar kilomita 235 ciki sa’a guda.