✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwa ta kashe mutum daya, ta rusa gidaje 32 a Kano

Wata guguwa da mamakon ruwan sama sun yi sanadin rasuwar mutum daya rushewar gidaje 32 a kauyen ’Yan Tsagai da ke Karamar Hukumar Rano ta…

Wata guguwa da mamakon ruwan sama sun yi sanadin rasuwar mutum daya rushewar gidaje 32 a kauyen ’Yan Tsagai da ke Karamar Hukumar Rano ta Jihar Kano.

Shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) Dokta Sale Jili ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis.

Ya kuma ce mutane da dama sun rasa muhallansu, wanda hakan ya sanya wasunsu neman matsuguni a gidajen makwabta da ’yan uwa.

Jili ya kuma ce hukumar ta jibge ma’aikatanta a kauyen domin ragewa mutane radadin asarar da hakan ya jawo musu.

“Mun ziyarci kauyen Tsagai kuma mun raba tallafi ga wadanda lamarin ya ritsa da su, mun raba buhunan shinkafa 30, na masara 30, na wake 30, na siminti 30 da kuma kwanon rufi da kusoshi,” inji shi.

Sauran kayayyakin da hukumar ta ce ta raba sun hada da botikan roba da cokula da man gyada da katifu da tumatirin gwangwani da kuma sinadaran dandanon girki.

Jili ya shawarci al’ummar yankin da su dinga kula da gyara magudanun ruwansu da shara, tare da gargadinsu kan gina gidaje a kan magudanun ruwa domin gujewa aukuwar makamancin lamarin a gaba.