Wasu daga cikin ’yan Majalisar Wakilai sun ‘saba’ alkawarin da suka yi na sadaukar da albashinsu na wata biyu domin taimakawa wajen yakar annobar coronavirus.
Hakan dai ya faru ne bayan da tuni wasu daga cikin ’yan majalissar suka tabbatar da cewar albashin su ya shiga asusun ajiyarsu da ke bankuna daban daban tun ranar Talata.
Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ne dai ya bayyana alkawarin da ’yanmajalisar suka yi na ba da tallafin albashin a wani sakon bidoyo, inda ya bayana karara cewa za su fara biya daga watan Maris.
Sai dai wata majiya ta ce majalisar ta dage cika alkawarin zuwa watannin Afrilu da Mayu sakamakon wannan akasin da aka samu.
- Darussa uku da Najeriya ka iya koya daga annobar coronavirus
- COVID-19: A bar mutum 12 su yi sallar Juma’a —Shaikh Dahiru Bauchi
Wani daga cikin ’yan majalisar ya bayyana wa wakilinmu cewar hakan ka iya faruwa ne sakamakon sabanin fahimta a tsakanin shuwagabannin majalisar da ofishin gudanarwa na majalissar.
Solomon Maren dan majalisa ne a karkashin tutar jam’iyyar PDP da ke wakiltar jihar Filato, kuma ya tabbatar wa wakilinmu cewa tabbas ya samu albashinsa.
Ya kuma kara da cewa hakan ya yi matukar ba shi mamaki duba da alkawarin da suka yi na sadaukar da albashin na watannin biyu.
Maren ya ce, “Da na tuntubi Kakakin Majalisa sai ya bayyana mani cewar Akawun Majalisa ya fada masa (Kakakin Majalisa) cewa ba za su iya ware albashinmu na watan Afrilu ba saboda bankunan sun rigaya sun fara tura albashin zuwa asusun mu.
“Tun da ba zai yiwu a ciro kudaden daga asusun mu ba, ya zama dole a yi mana lamuni a cire daga cikin na watannin Mayu da na Maris”, inji dan majalisar.
A nashi bayanin, mai magana da yawun Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, cewa ya yi laifin rashin cika alkawarin ba na ’yan majalisar ba ne.
“Idan masu alhakin biyan albashin sun samu matsalar aiwatarwa ai bai kamata a alakanta matsalar da mu ba. Ya kamata a fahimci cewa ’yar karamar matsala ce ta biyan kudin wadda kuma za a shawo kanta cikin gaggawa domin mu cika alkawarin taimaka wa gwamnatin tarayya domin ganin an shawo kan annobar Covid-19”.
Da ma dai wasu ’yan Najeriya sun soki matakin na ’yan majalisa suna cewa tun da albashinnsu ba taka kara ya karya bai dan aka kwatanta da alawus-alawus din da suke karba, kamata ya yi wakilan na jama’a su sadaukar da alawus-alawus din.