Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya sanar da rage yawan tawagar wakilan ƙasar da za su halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka.
Za dai a gudanar da taron na MDD karo na 79 a birnin New York na Amurka a cikin watan Satumba mai zuwa.
- Masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a Afirka — AU
- A gaggauta ceto ɗalibai 20 da aka sace a Benuwe — Majalisa
Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan ranar Asabar.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya ambato Gbajabiamila na sanar da umarnin a lokacin wani taron bita da fadar shugaban ƙasar ta shirya wa shugabannin hukumomin gwamnati da ke ƙarƙashin kulawar fadar.
Gbajabiamila ya ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa a lokacin tafiye-tafiyen jami’an gwamnatin.
Da yake ƙarin haske kan ƙudurin, ya ce Fadar Shugaban Kasar da hukumomin da ke ƙarƙashin kulawarta, na gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka da ƙa’ida, da kuma bin umarnin shugaban ƙasar, Gbajabiamila ya ce shugaban ya ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da ingantaccen tsari wajen gudanar da gwamnatinsa
“Na tattauna da shugaban ƙasa kan wannan, kuma ya sanar da ni cewa za mu ga haka cikin makonni masu zuwa lokacin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York.
Mista Gbajabiamila ya ƙara da cewa a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a ƙasar, an yi maganar rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa, don haka ya ce yanzu kowa na jiran ganin yawan tawagar da Nijeriya za ta je da ita taron na Majalisar Ɗinkin Duniya.
“A baya mun sani cewa, wasu na amfani da taron wajen tafiya harkokinsu na ƙashin kai.
“Saboda haka ne shugaban ƙasa ya bayar da umarnin cewa, a wannan karon duk wanda ba shi da abin yi a taron, to kada ya kuskura ya shigar tawagarmu zuwa Amurka, wannan shi ne umarnin Shugaban ƙasa,’’ inji Gbajabiamila.