Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya buƙaci gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, da ya bi umarnin kotu na dakatar da gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar gobe.
A ranar 22 ga Oktoba, 2024 ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta hana Sani Malumfashi, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 26 ga Oktoba.
A hukuncin da ya yanke, Simon Amobede, shugaban alƙalin kotun, ya ce Malumfashi bai cancanci gudanar da zaɓen jihar ba saboda “shi ɗan jam’iyyar NNPP ne mai ɗauke da katin jam’iyyar.
Sai dai da yake jawabi a ranar Alhamis yayin da yake miƙa tutoci ga ‘yan takarar jam’iyyar NNPP a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, Gwamna Yusuf ya ce babu wanda zai iya hana Hukumar zaɓe ta KANSIEC gudanar da zaɓen a wannan Asabar.
Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya gargaɗi gwamna Yusuf da ya daina ɗaukar duk wani mataki da zai daƙile doka da oda a jihar.
Jam’iyyar APC ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bi umarnin kotu, inda ta yi nuni da cewa kiran da gwamnan ya yi wa magoya bayan jam’iyyar NNPP da su yi watsi da umarnin kotun, wani lamari ne ƙarara na kiran tashin hankali da karya doka.