Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya bukaci daukacin al’ummar musulmi da su yi rokon ruwa tare da addu’ar wanzuwar zaman lafiya don habaka harkar noma a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani sakon barka da sallah, inda ya bukaci jama’ar jihar da kasance masu afuwa da kuma sada zumunci a tsakaninsu.
- Asalin al’adar Tuwon Sallah a kasar Hausa
- ‘Karawa sarakuna albashi a Gombe abu ne da aka dade ana jira’
Kazalika, gwamnan ya gargadi mutane kan muhimmancin bin matakan kare kai daga cutar COVID-19 da ke barazanar barkewa a karo na uku.
Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da irin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki sakamakon bullar cutar COVID-19, wanda ta shafi duniya baki daya.
Gwamnan ya ce za su ci gaba sa agaza wa jama’a ta hanyar ba su tallafi don rage musu radadin halin da suke ciki.
Har wa yau, ya ja hankali kan muhimmancin wanzar da zaman lafiya kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a tsakanin al’umma.
Ya umarci al’ummar jihar da su yi amfani da damar bukukuwan sallah babba don sada zumunci a tsakaninsu ba tare da la’akari da banbancin addini ko kabila ba.
“Zan yi amfani da wannan dama don ba ku tabbacin cewa gwamnatina za ta ci gaba da bunkasa harkar ilimi, lafiya, matasa, noma da sauransu.
“Za mu ci gaba da samar da manyan ayyuka da za su bunkasa tare da habaka rayuwar jama’ar Bauchi,” a cewarsa.
Sannan ya roki masu ababen hawa da su kasance masu bin dokokin hanya, musamman a lokutan bikin sallah don gujewa faruwar hatsari.