A ranar Juma’a shahararren Kamfanin Fasahar Zamanin nan Google, ya yi bikin karrama shinkafa dahuwar dafa-duka da aka fi sani da ‘Jollof rice’ a Turance.
Dafa-duka na daya daga cikin galibin nau’ikan abincin da ake sarrafawa a yankin Afirka ta Yamma.
Dafa-duka shinkafa ce da akan sarrafa ta hanyar cakuda duk kayan hade-hade a cikin tukunya daya.
Duk da dai ana samun dafa-duka a kusan duka kasashen Afirka ta Yamma, sai dai kuma dafa-dukan da ta fi shahara ita ce irin ta Najeriya da Ghana da Sierra Leone da Liberia da Kamaru.
Nau’ikan dafa-dukan da suka fi shahara a Najeriya sun hada da; dafa-dukan da ake girkawa a lokacin bukukuwan Kirsimeti (Chrismas Jollof Rice) da dafa-dukan Owanbe (Owanbe Jollof Rice) da kuma dafa-dukan ‘Concoction’.