A yau ne tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya marigayi Rashidi Yekini ya cika shekaru 60 da haihuwa, wanda ya kasance daya daka cikin manyan ‘yan wasan da aka yi a nahiyar Afrika, musamman idan aka yi la’akari da yadda ya zura kwallaye a raga.
Duk da cewa ya rasu a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 2012 yana da shekaru 48, amma har yanzu miliyoyin mutane na tunawa da irin gudunmuwar da ya bayar.
- Najeriya ta yi galaba kan kamfanin P&ID a shari’ar bashin dala biliyan 11
- Za mu fara bai wa dalibai rancen kudin karatu a watan Janairu — Tinubu
Kamfanin Google na daga cikin wadanda suka karrama tsohon dan wasan a wannan ranar ta cikarsa shearu 60, inda suka sanya hotonsa na murnar cin kwallonsa a gasar lashe kofin duniya ta shekarar 1994.
Zanen na Google ya kwatanta murnar da Yekini ya yi lokacin da ya ci wa Najeriya ƙwallonta ta farko a gasar cin kofin duniya a 1994.
Hakan ya nuna lokacin da Yekini ya zura ƙwallo a ragar Bulgeriya, ya shige cikin ragar tare da kama ta da hannu bibbiyu yayin da hawayen murna ke kwararo masa.
Wasu rahotanni sun ce, Yekini wanda haifaffen Jihar Kaduna ne, gabanin rasuwarsa ya faɗa ƙangin talauci da rashin matsuguni bayan yin fice a matsayin ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na Najeriya.
Bari mu yi duba kan wasu daga cikin nasarori 10 da dan wasan ya samu a lokacin rayuwarsa:
1 Yakini ya fara kwallonsa ne da kungiyar kwallon kafa ta UNTL FC da ke Kaduna.
2 A shekarar 1982 ya koma kungiyar Shooting Stars, inda ya kwashe tsawon shekaru 2 kuma ya samu nasarar zura mata kwallaye 45 a cikin wasanni 53 da yayi mata.
3 Rashidi Yekini, ya zamo dan wasan Najeriya na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara na Afrika, a shekarar 1993.
4 Tsohon dan wasan ya kuma jagoranci kungiyar Shooting Stars wajen kaiwa wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Afrika a shekarar 1984.
5 Haka nan, Yekini ya buga wasanni a kasashen Spain da Tanzania da Saudiya da Tunisia da Girka da Portugal da kuma Switzerland.
6 A kakar wasan shekarar 1993 zuwa 1994, Yakini ya lashe kyautar dan wasan da yafi zura kwallo a gasar Portugal lokacin ya na kungiyar Vitoria Setubal, inda ya zura kwallaye 21.
7 Yekini ya taka rawar gani a tawagar kasarsa ta Najeriya, wajen samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 1994, kuma ya zura wa tawagar kwallon farko a gasar.
8 Shekaru sama da 14 tsohon dan wasan ya kwashe da tawagar Najeriya, lamarin da ya bashi damar sake komawa gasar lashe kofin duniya ta 1998.
9 A wasanni 58 da ya bugawa kasarsa, Yekini ya zura kwallaye 37, inda har yanzu babu wani dan wasa a tarihin kasar da ya zura mata kwallaye kamarsa.
10 Dan wasan ya auri mata uku yana kuma da ‘ya’ya uku, Yemisi da Omoyemo da kuma Damilola.