Gwamnatin Jihar Gombe ta ce ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya don samar da ruwan sha.
Yarjejeniyar ta jobanci hada gwiwa a tsakanin gwamnatocin biyu don samar da kudin da ake bukata don inganta da fadada Shirin Samar da Ruwa na Yankin Gombe.
- Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano
- Amarya Ta Farfado Bayan An Binne Ta A Kabari
A wata sanarwa da ya fitar, Daraktan Al’amuran Yada Labarai na Jihar ta Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya ce manufar yarjejeniyar ita ce gyarawa da fadada Shirin, wanda zai rika samar da lita miliyan 50 ta ruwa a kowace rana
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar, yayin da Ministan Ruwa Injiniya Sulaiman Adamu ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya.