“Bari .dukan duniya ta rera wakar farin ciki ga Ubangiji! Ku yi wa Ubangiji sujada da murna, Ku zo gabanSa, kuna rera wakokin farin ciki! Kada fa a manta da cewa, Ubangiji Shi ne Allah! Shi ne Ya yi mu, mu kuwa naSa ne, Mu jama’arSa ne, mu garkenSa ne. Ku shiga haikalinSa da godiya, Ku shiga wurinSa Mai tsarki, ku yabe Shi! Ku gode maSa, ku yabe Shi! Ubangiji Nagari ne, kaunarSa madauwamiya ce, AmincinSa kuwa har abada abadin ne.” Zabura 100
Barkanmu da sake haduwa, godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka domin yawan alheranSa da Ya bar mu da rai har muka ga wannan sabon wata. Ba da ikon kanmu ba ne ko iliminmu da karfinmu, amma domin kaunarSa mara iyaka.
Wannan batu “Godiya” ba sabo ba ne a gare mu, mun sha tattaunawa kan kalmar godiya ga Ubangiji Allah. A wannan makon, za mu ga wasu ayoyi cikin Littafi Mai tsarki da zai taimake mu wajen yin nazari a kan gode wa Allah.
Muna nuna godiyarmu ga Ubangiji cikin kowace hali. 1 Tasalonikawa 5:18, “Ku yi godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.”
A lokuta da dama nakan ji mutane na guna-guni a kan wasu abubuwa da ba su da iko a kai, misali, lokacin sanyi ko zafi, sai ka ji suna ta guna-guni cewa sanyin nan ya yi yawa ko zafin nan ya yi yawa. Da damina ko rani, ruwan sama ya yi yawa ko rashin ruwan nan ya yi yawa. Mu sani fa Littafi Mai tsarki ya fadi cewa akwai lokaci domin komai cikin duniya idan muka karanta Littafin Mai Hadisi 3:1-9. Idan fa haka ne, me ya sa yakan zama mana da wuya mu gode wa Ubangiji a irin wannan lokuta? Littafi Mai tsarki na cewa mu zama masu godiya ga Ubangiji cikin kowane irin hali da muka tarar da kanmu a ciki amma ba mu zama masu guna-guni ba. Ai ko mu mutane ma idan wani ya nuna mana godiyarsa don wani abin da muka yi masa komai kankantarsa mukan ji dadi matuka, mukan ji kamar mu dada masa in da hali kuma sai ka ga wani kan iya kara bashi dadi a kan abin da ya bayar. Hakan nan Ubangiji Yake so mu zama, masu godiya a koyaushe. Bari mu dubi wasu ayoyi cikin Littafi Mai tsarki da ke magana a kan wannan darasi, sai mu yi binbinni a kai, muna yi wa Ubangiji yabo da godiya.
Zabura 92:1-5, 136:1-9, 118:1-5,
Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya, a rera waka don girmanSa, Allah Mafi daukaka,
A yi shelar madauwamiyar kaunarka kowace safiya, AmincinKa kuma kowane maraice,
Da abubuwan kade-kade masu tsarkiya, Da amon garaya mai dadi.
Ya Ubangiji, AyyukanKa masu iko suna sa ni murna, Saboda abin da Ka aikata Ina rera waka domin farin ciki. AyyukanKa da girma suke, ya Ubangiji! TunaninKa da zurfi suke!
Ku gode wa Allahn da Ya fi dukan alloli girma, Gama kaunarSa madauwamiya ce.
Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji, Gama kaunarsa madauwamiya ce.
Shi kadai ne Yake aikata mu’ujizoji masu girma, Gama kaunarsa madauwamiya ce.
Ta wurin hikimarSa Ya halicci sammai, Gama kaunarsa madauwamiya ce.
Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi, Gama kaunarsa madauwamiya ce.
Shi ne Ya halicci rana da wata, Gama kaunarsa madauwamiya ce,
Rana don ta yi mulkin yini, Gama kaunarsa madauwamiya ce,
Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare, Gama kaunarsa madauwamiya ce.
Ku gode wa Ubangiji, Domin Shi Mai alheri ne, kaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
Bari jama’ar Isra’ila su ce, “kaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
Bari dukan firistoci na Allah su ce, “kaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
Bari dukan wadanda suke tsoronSa su ce, “kaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji Ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni.
Filibiyawa 4:6-7,
Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.
Kada fa ka jira sai wani abin alheri ya same ka kafin ka gode wa Ubangiji Allahnka, ai a zamanSa na Ubangiji Mai halittar komai da kowa, Mai iko duka, Masanin komai har ma zurfin zukatan dan Adam, Mai rike da ikon rai da mutuwa, Mai biyan bukata, Madogaranmu, Allah Mai girma, ai ba sai an gaya maka ba. Zabura 14:1, Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!” Abubuwan da ke kewaye da mu kadai ma sun shaida alheranSa zuwa gare mu, domin duk abin da Ya halitta dominmu ne. Ya albarkace mu da iska don mu shaka da ruwa da kasa da rana da dabbobi da itatuwa da sauransu, to, me ya fi haka? Ko kana gani arzikinka zai sayi wadannan abubuwa? Ai wannan kadai ya isa mu gode maSa.
Mu yabi Ubangiji.
Shalom.