✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Zidane zai fara wasansa na farko a Madrid

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu, tsohon dan kwallon Real Madrid na Sifen zai fara horarwa a wasansa na farko a kulob din…

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu, tsohon dan kwallon Real Madrid na Sifen zai fara horarwa a wasansa na farko a kulob din Madrid na Sifen tun bayan da aka zabe shi koci a ranar Litinin da ta gabata.
Idan za a tuna a ranar Litinin da ta wuce ne kulob din Madrid ya zabe shi jim kadan bayan kulob din ya kori tsohon kocinsa Rafa Benitez.
 Madrid dai za ta kara da kulob din Deportibo La-Coruna a gasar La-Liga ta Sifen ne a gobe Asabar kuma shi ne zai kasance wasan Zidane na farko a matsayinsa na kocin kulob din.
Wasan zai gudana ne a filin wasan Madrid Santiago Bernebeu da misalin karfe takwas da rabi na dare agogon Najeriya.
Masu goyon bayan kulob din da masana harkar kwallo sun zuba ido su ga yadda kocin zai nuna basirarsa a wasan goben.