✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a yi karon-battar birnin Manchester tsakanin United da City

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a fafata karon-battar birnin Manchester a tsakanin Man United da Man. City a ci gaba da…

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a fafata karon-battar birnin Manchester a tsakanin Man United da Man. City a ci gaba da fafatawa a gasar rukunin Premier ta kasar Ingila. Wannan shi ne wasa karo na hudu bayan da aka fara gasar a watan jiya.
Wasan na kece raini a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da makwabciyarta ta Manchester City a filin wasa na Old Trafford, za a fafata wasan ne da misalin karfe 12:30 na rana agogon Najeriya.
An yi hasashen wasan zai yi zafi ne bayan da kungiyoyin biyu suka yi sababbin masu horarwa.  Yayin da kulob din Manchester United ya dauki Jose Mourinho a matsayin kocinsa, shi kuwa kulob din Manchester City ya dauki Pep Guardiola ne a matsayin koci.  Manajojin biyu sun gwada kwanji a gasar La Liga ta kasar Sifen.  A wancan lokaci Mourinho yana horar da kulob din Real Madrid ne yayin da Guardiola kuma yake horar da kulob din FC Barcelona.
Kawo yanzu kungiyar Manchester City ce take saman teburin gasar da maki 9 sai kulob din Chelsea a matsayi na biyu sai kuma kulob din Manchester United a matsayi na uku.  Sai dai dukkan kungiyoyin uku sun hada maki tara-tara ne amma yawan cin kwallaye ne ya bambanta su.
 Ana sa ran gidajen kallon kwallo musamman a Najeriya za su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya.  Yayin da wadansu magoya baya ke ganin Manchester United ce za ta samu nasara a wasan, wadansu kuma cewa suke yi Manchester City ce za ta bi United har gida ta yi mata sakiyar da babu ruwa.