✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a mika kofin firimiya ga Leicester City

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a mika kofin firimiya na Ingila ga kulob din Leicester City bayan ya lashe gasar a…

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a mika kofin firimiya na Ingila ga kulob din Leicester City bayan ya lashe gasar a karon farko a shekaru 132 da kafa kulob din.
Leicester City dai ta samu nasarar lashe gasar rukuni-rukuni na Ingila ne da aka fi sani da firimiya bayan ta tashi wasa canjarasa (0-0) da kulob din Manchester United a ranar Lahadin da ta wuce yayin da kulob din Tottenham kuma ya yi kunnen doki 2-2 da na Chelsea a ranar Litinin da ta gabata da hakan ya sa ta ba kulob din Tottenham tazarar maki bakwai ana saura wasanni biyu a kammala gasar.
A wasan da kulob din Leicester zai yi da na Eberton a gobe Asabar da misalin karfe 5 da rabi na yamma agogon Najeriya ne za a mika wa kulob din kofin gasar firimiya da zarar an kammala wasan.  Lashe wannan kofi ya sa kulob din ya kafa sabon tarihi a gasar, bayan ya kwashe shekara 132 ba tare da ya taba lashe kofin ba sai a wannan karo.
Masana harkar kwallo suna ganin lashe kofin da Leicester ta yi ya zama tamkar almara ganin yadda suka yi ba-zata duk da kasancewar manyan kulob da ke fafatawa a gasar amma sai da suka ba marada kunya.
Kulob din ya lashe gasar ce bayan ya hada maki 77 daga cikin wasanni 36 yayin da kulob din Tottenham yake biye da maki 70 sai na Arsenal da ke matsayi na uku da maki 67 sai na Manchester City da ke da maki 64.
Tuni kulob da dama suka fara rububin ’yan kwallon Leicester don ganin sun dauke su kafin a fara kakar wasa mai zuwa, sai dai kocinsu Claudio Raneri ya hore su kada su yi gaggawar barin kulob din musamman a wannan lokaci da suka kafa sabon tarihi a gasar firimiyar Ingila.