✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a gwabza a tsakanin Chelsea da Man United

A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin Firmiya na Ingila, a gobe Asabar idan Allah Ya kai mu ne za a yi wasa mai…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin Firmiya na Ingila, a gobe Asabar idan Allah Ya kai mu ne za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Chelsea da na Manchester United.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 12:30 na rana agogon Najeriya a filin Chelsea na Stamford Bridge.

Za a yi wasan ne a tsakanin kulob din da ke matsayi na 2 a teburin gasar wato Chelsea da kuma Man United da ke matsayi na 8.  Kawo yanzu an yi wasanni 8 kuma wannan shi ne wasa na 9 tun  da aka fara gasar a kakar wasa ta bana.

Akwai yiwuwar Chelsea ta dare teburin gasar idan ta samu nasara a wasan. Ita kuma Manchester United za ta iya farfadowa daga tangal-tangal din da take yi ne a wannan gasa idan ta samu nasara.

Sai dai rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna an dage kocin United Jose Mourinho daga tsayawa a kusa da fili  saboda wasu kalaman batunci da ya yi a lokacin da Man United ta yi wasa da Newcastle United inda United ta samu nasara da ci 3-2 kimanin mako biyu da suka wuce.

Ke nan Mourinho zai zauna ne a wajen ’yan kallo yayin da mataimakinsa zai gaje shi a wajen tsayawa a kusa da filin kwallon don kula da ’yan kwallon United a yayin wasan.

A bana Mourinho yana shan suka musamman a wajen magoya bayan kulob din United ganin yadda kulob din yake tangala-tangal a kakar wasa ta bana.

Chelsea dai tana tashe a kakar wasa ta bana, don kawo yanzu ba ta samu rashin nasara ko daya ba, amma United ta samu rashin nasara har sau biyu.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika da masoya kwallon kafa don ganin yadda wasan zai kaya.