✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara rigakafin cutar Shan Inna a Jihar Kaduna

Hukumar Kula da Kiwon Lafiya daga Tushe ta Jihar Kaduna (SPHCDA) ta bayyana cewa daga gobe Asabar za a fara gudanar da rigakafin cutar shan…

Hukumar Kula da Kiwon Lafiya daga Tushe ta Jihar Kaduna (SPHCDA) ta bayyana cewa daga gobe Asabar za a fara gudanar da rigakafin cutar shan inna na kwana uku a kammala a ranar 16 ga Afrilun nan a duk fadin jihar.

Allurar rigakafin wani kokari ne da hukumar ke yi don ganin ta cimma kashi 85 cikin na wadanda za a yi wa rigakafin cutar shan innar.

Mataimakin Daraktan Hukumar, Hamza Ibrahim-Hamza ya bayyana wa manema labarai cewa za a yi rigakafin ne a dukkan kananan hukumomin Jihar Kaduna 23.

Hamza ya bayyana cewa hukumar za ta nemi taimakon sarakunan gargajiya da hakimai da shugabannin addinai wajen ganin aikin rigakafin ya samu nasara, musamman wajen zakulo kananan yara wadanda shekarunsu suka kama daga daya zuwa biyar.

Ya ce hukumar ta aika akalla ma’aikatan lafiya biyu zuwa kauyuka masu nisa, kuma za a yi rigakafin ne ta hanyar bi gida-gida da asibitoci, sannan za a samar da karin kayan aiki don gudanar da aikin cikin nasara. Malam Hamza ya roki iyayen yara su masu gudanar da allurar rigakafin hadin kai don ganin an cimma nasara.