✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar firimiyar Najeriya

A gobe Asabar idan Alah Ya kaimu ake sa ran za a fara gudanar da gasar rukunin firimiya ta Najeriya.  Yayin da sassan duniya ciki…

A gobe Asabar idan Alah Ya kaimu ake sa ran za a fara gudanar da gasar rukunin firimiya ta Najeriya.  Yayin da sassan duniya ciki har da Nahiyar Turai suka shiga zagaye na biyu a gasannin kasashensu a Najeriya kuwa sai a gobe za a fara gudanar da gasar a kakar wasa ta bana (2018/2019).

Sai dai kulob din Katsina United da na Kano Pillars ne kadai za su fafata a gobe amma sauran wasannin sai jibi Lahadi ne za a gudanar da su.

Kulob 20 ne za su fafata a wannan gasa.  Idan za a tuna kulob din Filato United ne ya lashe gasar a bara bayan ya shafe shekaru masu yawa ba tare da samun nasarar hakan ba, don haka masana harkar kwallo suna ganin kulob din zai fuskanci turjiya daga abokan karawarsa da ke neman kwace kofin a bana saboda sai kulob din ya yi da gaske muddin yana son lashe kofin a karo na biyu a jere.

  Kulob uku ne suka samu koma-baya (relegation) a bara da suka hada da Abubakar Bukola Saraki (ABS) Babes da ke Ilorin da Gombe United da kuma kulob din Remo Stars na Akure.

Kulob uku da suka samu nasarar hayewa gasar a bana sun hada da Go Round da ke Jihar Ribas da Katsina United da kuma Yobe Stars.

Tuni Hukumar da ke kula da gasar (NPFL) ta ce ta shirya tsaf don tunkarar gasar, kuma ta hori wadanda za su fafata a gasar da su yi kokarin bin doka da oda.