✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara Gasar Cin Kofin Duniya na U-17

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a fara Gasar Cin Kofin Duniya na Matasa ’Yan Kasa da shekara 17 a Brazil.  Gasar…

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a fara Gasar Cin Kofin Duniya na Matasa ’Yan Kasa da shekara 17 a Brazil.  Gasar wacce ke gudana duk bayan shekara biyu, a bana za a yi ta ce a kasar Brazil.

Ana sa ran kasashe 24 daga kowane bangare na duniya ne za su fafata inda za a dauki tsawon mako uku ana yi.

Kasashe hudu ne za su wakilci Nahiyar Afirka a wannan gasa da suka hada da Najeriya da Angola da Senegal da kuma Kamaru.

Najeriya ce ta fi yawan lashe wannan kofi a tarihi inda ta dauka har sau biyar. Ta fara dauka ne a 1985 sai a 1993 sai a 2007 sai a 2013 sai kuma a 2015.

Sai Brazil ke biye da ita inda ta dauka sau 3 sai kasashen Ghana da Meziko da suka taba dauka sau bibbiyu.

Najeriya da Ghana ne suka taba lashe wannan kofi daga Nahiyar Afirka a tarihin gasar.

Najeriya za ta fafata a Rukunin B da kasashen Hungary da Ecuador da Austireliya inda kasashe biyu da ke saman tebur a kowane rukuni  za su haye matakin zagaye na biyu.

An fara gasar ce tun a 1985 kuma ake ci gaba da gudanar da ita duk bayan shekara biyu a kasashe daban-daban inda a wannan karo Brazil za ta karbi bakunci.

Masoya kwallon kafa a sassan duniya sun zuba ido su ga yadda gasar za ta gudana ciki har da na kungiyar  Golden Eaglets ta Najeriya.

Fatarmu Allah Ya ba Najeriya sa’a ta lashe kofin a karo na 6.