✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara Gasar cin kofin CHAN a Maroko

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a fara gudanar da gasar cin kofin Afirka na masu yin kwallo a gida…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a fara gudanar da gasar cin kofin Afirka na masu yin kwallo a gida da ake wa lakabi da CHAN.

Gasar ita ce karo na biyar tun wacce aka fara a shekarar 2009 a kasar Kwaddebuwa.  Kuma ana gudnaar da gasar ce duk bayan shekara biyu.  Don haka Kwaddebuwa ce ta dauki nauyi a shekarar 2009 inda Dimokuradiyyar Kongo ta lashe kofin bayan ta lallasa Ghana a wasan karshe da ci biyu babu ko daya.  Sai a shekarar 2011 kasar Sudan inda Tunisiya ta lashe kofin bayan ta lallasa Angola da ci 3-0.  Sai a shekarar 2014 inda Afirka ta Kudu ta dauki nauyi inda Libya ta lashe kofin bayan ta lallasa Ghana a bugun fanariti da ci 4-3.  Sai shekarar 2016 da Ruwanda ta dauki nauyi inda Dimokuradiyyar Kongo ta lashe kofin bayan ta lallasa Mali ci 3-0 a wasan karshe.

  kasashe 16 ne za su fafata a bana da suka hada da mai masaukin baki Maroko da Mauritania  Kwaddebuwa da Namibia da Guinea da Sudan da Kwaddebuwa da Namibiya.  Sauran kasashen sun hada Zambiya da Uganda da Najeriya da Ruwanda.  Sauran su ne Angola da Burkina Faso da Kamaru da Kongo da Libya da Ekuatorial Guinea.

Za a yi gasar ta bana ne a tsakanin ranakun 12 ga watan Janairu zuwa 4 ga Fabrairun 2018.