✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a ci gaba da Gasar La-Liga

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni ta kasar Sifen (La-Liga) bayan…

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni ta kasar Sifen (La-Liga) bayan an yi hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

A Nahiyar Turai, a kasar Ingila ne kadai ba a yi hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara ba, inda a tsakankanin nan an buga wasannin da dama a gasar ta firimiya.

Wasannin La-Liga da za a yi a gobe sun hada da na Atletico Madrid da Getafe da misalin karfe 1 na rana agogon Najeriya sai balancia da Girona da karfe 4 da kwata na yamma sai kuma Sebilla da Real Betis da misalin karfe 8 da minti 45 na dare.

A jibi Lahadi kuma wasanni masu zafi sun hada da na FC Barcelona da Lebante da misalin karfe 4 da kwata na yamma sai kuma Celta bigo da Real Madrid da misalin karfe 8 da minti 45 na dare agogon Najeriya.

Kawo yanzu FC Barcelona ce take saman teburin gasar da maki 45 a wasanni 17 sai Atletico Madrid mai maki 36 sai balencia mai maki 34 sai Real Madrid mai maki 31 sai dai tana da kwantan wasa daya.