A gobe Asabar za a kammala makon wasanni na Makarantar Sakandaren sojoji ta NMS karo na uku.
Makon wasannin, wanda aka fara a ranar Litinin da ta gabata, inda dalibai za su fafata a fagen wasannin daban-daban.
Da yake jawabi a wajen bude bukin wasannin, Daraktan Wasanni da Motsa Jiki na Rundunar Sojan Kasa ta Najeriya, Manjo Janar Okpe Wilson Ali, wadda Kwamandan Makarantar Motsa Jiki ta Sojan Kasa da ke Zariya, Birgediya Janar Adebisi Kolejaiye ta wakilta ya bayyana cewar motsa jiki a aikin soja da karatu na da muhimmanci.
Ya ci gaba da cewa makarantar NMS ta yi fice a fagen wasanni ta hanyar lashe lambobin yabo.
Ya Kuma yaba wa Kwamandan makarantar bisa yadda ya jajirce wajen tabbatar da ci gaban wasanni a makarantar.
Da ya juya kan dalibai kuwa, sai ya shawarce su da su kasance masu da’a da bin dokokin wasanni.
Shi ma da ya ke jawabi Kwamandan makarantar Manjo Janar M. M. Bunza ya ce tsoffin daliban makarantar sun yi fice a fagen wasanni a ciki da wajen Najeriya. Ya Kuma tabbatar da cewa makarantar za ta ci gaba da kasancewa a sahun gaba a fagen wasanni tare da goyon baya mahukunta makarantar.