✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Najeriya za ta yi wasa da Bosniya-Herzegobina

A gobe Asabar, idan Allah Ya kaimu, kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles za ta yi wasanta na biyu da Bosniya Herzegobina a ci…

 ’Yan kwallon Najeriya a lokacin fafatawarsu da Iran a ranar Litinin.  An tashi wasan ne 0-0A gobe Asabar, idan Allah Ya kaimu, kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles za ta yi wasanta na biyu da Bosniya Herzegobina a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil. Za a yi wasan ne da misalin karfe goma sha daya na dare agogon Najeriya.
A wasan da Najeriya ta yi na farko da Iran a ranar Litinin da ta wuce, an tashi ne babu ci watau 0-0 don haka akwai bukatar Najeriya ta samu nasara a wannan karon don a cigaba da damawa da ita a gasar.
Idan Najeriya ta samu nasara, zai kasnace ta hada maki hudu kenan daga wasanni biyu amma idan ta samu akasin haka, to za ta tashi da maki daya ne kacal daga wasanni biyu.
Wasan zai yi zafi don ganin kasar Bosniya ma tana neman samun nasara ne bayan Ajantina ta lallasa ta da ci 2-1 a wasanta na farko.
Ita kuma Ajantina za ta yi wasanta na biyu ne da Iran a goben da misalin karfe biyar na yamma.  Shi ma wasa ne da zai yi zafi don duk kasashen biyu suna bukatar samun nasara ne.  Idan Ajantina ta samu nasara ko shakka babu ta haye zagaye na biyu a gasar  tun da za ta hada maki shida daga wasanni biyu kenan yayin da ita kuma Iran idan ta samu nasara za ta hada maki hudu daga wasanni biyu.
Ko ma dai yaya wasannin za su kaya magoya bayan kwallon kafa sun zuba ido don kashe kwarkwatar idanu.