✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Jami’ar Usman Danfodiyo za ta yi bikin yaye dalibai 12,282

Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato ta shirya domin gudanar da yaye dalibanta dubu 12 da 282 tare da karrama wadansu fitattun mutane da…

Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato ta shirya domin gudanar da yaye dalibanta dubu 12 da 282 tare da karrama wadansu fitattun mutane da suka ba da gudunmawa a bangaren gina al’umma su biyar, inda za ta ba su digirin digirgir na karramawa da za a yi a filin taro na jami’ar a gobe Asabar.

Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Audu Zuru ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai da ya kira kan  shirye-shiryen bikin da za a fara yau Juma’a, inda ya ce babban biki ne saboda shekara uku ba su yi ba.

“Ina farin cikin sanar da ku tsarin bikinmu ya kammala kuma za mu hade bikin yaye dalibai karo na 35 da 36 da 37, inda za mu yaye masu digiri da digiri na biyu da wadanda za mu karrama,” inji shi.

Ya ce, “Daliban za su karbi shaidarsu na samun horo da tarbiyya a jami’ar, kuma daga cikinsu mutum 135 ne suka kammala karatun digiri na uku, sai  770 suka kammala digiri na biyu, yayin da 96 suka karatun share fage na digiri na biyu, sai 10,994 masu digiri na farko da kuma 287 difiloma. Akwai dalibai 109 da za a bai wa kyaututtuka.”

Ya ce a cikin daliban, akwai 113 da suka samu nasara da babbar daraja (first class), sai 2,375 da  ke da matakin daraja ta biyu babban aji (second class upper), sai 6,603 matakin daraja ta biyu karamin aji (second class lower), yayin da 1,556 ke da matakin daraja ta uku (third class) sai 347 ne karshe.

Farfesa Abdullahi Zuru ya ce za su karrama mutum biyar, uku za a ba su digirin girmamawa da suka hada da Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar da Alhaji Muhammad Aliko Dangote da Sheikh Muhammad Mujtaba Isah Talatar Mafara. Biyun kuma tsofaffin shugabannin makarantar ne wato Sarkin Yawuri Dokta Muhammad Zayyanu Abdullahi da Farfesa Tijjani Muhammad Bande, inda za a ba su karramawar gogewa a  ilimi (Emeritus).