✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Golden Eagles za ta kece raini da Menas ta Nijar a Abuja

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta zabi gobe Asabar ta kasance ranar da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da…

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta zabi gobe Asabar ta kasance ranar da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da Golden Eaglets za ta fafata da takwararta ta Nijar da ake kira Menas a wasan neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka na ’yan kasa da shekara 17 da zai gudana a Madagascar a shekara mai zuwa (2017).
Golden Eaglets wacce ta lashe gasar cin kofin duniya na matasa sau biyar, bayan ta lashe karo na biyar a bara a Chile, an kasafta ta ne a wasa zagaye na biyu don ganin ta fafata a matakin neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi a Madagascar.
Idan za a tuna a bara, Golden Eaglets ce ta kasance ta biyu a gasar cin kofin matasa na Afirka da aka yi a Nijar, bayan kungiyar Menas ta Nijar ta lallasa ta da ci 2-0 a wasan da ya gudana a Niamey da ke Nijar, don haka wannan tamkar wata dama ce da yakamata kungiyar ta rama cin da Nijar din ta yi mata.
Sannan wannan wasa shi ne karo na hudu da kungiyoyin biyu suke haduwa a tsakanin shekaru hudu da suka wuce.
A shekaranjiya Laraba ne Golden Eaglets ta fafata a wasan sada zumunta da kungiyar Piloter Football Academy da ke garin Kaduna a filin wasa na Abuja a shirye-shiryen tunkarar Mendas ta Nijar a gobe Asabar.  Wannan shi ne wasa na bakwai da kungiyar take yi a matsayin sada zumunta da kungiyoyi daban-daban da ke kasar nan duk a shirye-shiryen tunkarar wasannin neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka da za a yi a Madagascar a badi.