A ci gaba da fafatawa a gasar Premier ta Ingila, a gobe Asabar za a buga wasa karo na 18. Kulob din Eberton zai kece-raini ne da na Arsenal da misalin karfe daya da rabi na rana agogon Najeriya. Da karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya kuma kulob din Manchester City zai shawo ta da na Leicester City.
A jibi Lahadi kuma kulob din Watford ne zai hadu da na Manchester United da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya yayin da Tottenham Hotspur zai yi gumurzu da kulob din Chelsea da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya. Wadannan ne wasanni mafiya zafi a wannan mako a gasar Premier ta Ingila kamar yadda jadawalin gasar ya nuna.