A gobe ne Rukunin Kamfanin Media Trust, masu jaridar Aminiya da Daily Trust da Talabijin din Trust TV da Trust Radio zai gudanar da muhawara a tsakanin ’yan takarar Gwamnan Kano.
Muhawarar za ta gudana ne a tsakanin ’yan takar guda hudu daga cikin ’yan takarar kujerar su takwas.
- Kokowar Ganduje, Kwankwaso da Shekarau wajen kwace Kano
- Canjin kudi: Gwamnonin APC sun yi wa Aso Rock tsinke
Muhawarar mai taken “Trust Nigeria 2023 Elections Debate” za ta bayar da dama ga jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da za su fafata a zaben shekarar 2023 don sanar da masu zabe irirn kudurce-kudurcen da suke da shirin aiwatarwa yayin da suka yi nasarar lashe zabe.
Tuni dai wadanda za su tattauna a muhawarar da suka hada da Nasir Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP da Mohammed Abacha na Jam’iyyar PDP da Bashir I. Bashir na Jam’iyyar LP sun nuna aimcewarsu da kasancewa a wajen wannan taro inda suka yi alkawarin sanar da masu zabe dalilansu na son zama Gwamnan Jihar Kano, jihar da aka san ta a matsayin cibiyar kasuwanci.
Babban Jami’in Gudanarwa na Rukunin Kamfanin Media Trust, Malam Munir Gwarzo ya bayyana cewa masu shirya taron sun sami tabbaci daga ’yan takara cewa muhawarar za ta mayar da hankali kan abubuwa da suka shafi al’umma kai-tsaye da suka hada da harkar ilimi da lafiya da kasuwanci da ayyukan gona da harkar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli da harkar gidaje da ayyukan ci gaba da kuma harkar gina rayuwar dan Adam.
Malam Munir Gwarzo ya kara da cewa za a gudanar da muhawarar ce a dakin taro na Tsangayar Harkokin Sadarwa na Jami’ar Bayero Kano da misalin karfe 10 na safe.
A cewarsa zabar harshen Ingilishi da aka yi don yin amfani da shi a muhawarar ya biyo bayan dalilai da dama da suka hada da matsayin jihar da kuma yanayin siyasar kasar da kuma yin duba da cewa al’ummar da ke wasu sassa na kasar da ma duniya gaba daya suna son sanin wanda zai zama Gwamnan Jihar a nan gaba.
Ya kuma bayyana cewa don tabbatarwa ba abar al’ummar jihar musamman wadanda ba su fahimci harshen Ingilishi a baya ba, masu shirya muhawarar sun tsara yadda za a gudanar da fassara da kuma sharhi kai-tsaye cikin harshen Hausa inda za a watsa shi ta kafafen watsa labarai na Rediyon Freedom da Nasara FM da Vision FM yayin da kuma za a sanya muhawarar kai-tsaye wato cikin harshen Ingilishi a kafafen sadarwa kamar Trust TV da kuma Gidan talbijin na Abubakar Rimi.
Har ila yau Mataimakin Babbn Edita na Kamfanin Media Trust Dokta Sulaiman Suleiman ne zai jagoranci muhawarar yayin da kuma Dokta Maude Gwadabe wanda shi ne Shugaban Sashen Hausa na Kamfanin Media Trust zai jagoranci yin sharhi cikin harshen Hausa.