✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar tankar mai ta kashe mutum 12 a Binuwai

Hadurran da ke aukuwa sakamakon fashewar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya.

Gawar mutum 12 aka tsinto wadanda suka rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi sakamakon fashewar tankar mai a garin Oshigbudu na Jihar Binuwai.

Tankar mai dauke da dakon man fetur ta fadi ne ranar Lahadi a kan hanyar zuwa Abuja daga garin Otukpe na Jihar Binuwai.

Bayan faduwar tankar man a tsakanin hanyar Oshigbudu zuwa Obagaji, man dake cikin ta ya kwarara kafin kamawa da wuta.

Shaidu sun ce motar wacce ta fadi da misalin karfe 1.00 na rana a sakamakon shanyewar birki ta kama da wuta kuma ta laso wasu shaguna da gidaje da ke kusa da wurin da hadarin ya faru.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura reshen jihar wanda ya inganta rahoton, ya tabbatar da mutuwar mutum 12 da suka kunshi maza takwas da mata biyu da kuma wani karamin yaro daya.

Kwamanda Yakubu Mohammed ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutum ya karu yayin da gawar mutum 12 da aka zakulo sun mutu ne a daidai lokacin aukuwar hadarin.

Hadurran da ke aukuwa sakamakon fashewar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya, inda wasu ke dora alhakin hakan a kan rashin kyawun hanyoyi.

Wani rahoto na BBC Hausa ya nuna cewa, a watan Yulin 2019, an samu akalla mutum 45 da suka mutu yayin da sama da 100 suka jikkata sakamakon hadarin fashewar tankar mai a yankin.