✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar bututun mai ta hallaka mutum biyu a Legas

Mutum biyu ne suka mutu yayin da wasu suka jikkata tare wasu motoci da dama suka kone kurmus a wutar da tashi sakamakon yoyon bututun…

Mutum biyu ne suka mutu yayin da wasu suka jikkata tare wasu motoci da dama suka kone kurmus a wutar da tashi sakamakon yoyon bututun man fetir a Ijegun a birnin Legas da safiyar yau Alhamis.

A cewar Hukumar Agajin Gaggagawa ta jihar Legas, LASMA, mutanen biyu da suka mutu su ne wadanda suka haddasa wutar a lokacin da suke kokarin arce wa jami’an tsaro bayan an gano suna kokarin satar man daga bututun man da ke yoyo.