✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: ‘Yan kwana-kwana sun kubutar da matashi a Kano

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta samu nasarar kubutar da wani matashi dan shekara 18 mai suna, Usman Muktar da safiyar ranar Laraba yayin…

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta samu nasarar kubutar da wani matashi dan shekara 18 mai suna, Usman Muktar da safiyar ranar Laraba yayin da wata gobara ta tashi a wani gidan sayar da iskar gas.

Jami’in hulda da al’umma na Hukumar, Alhaji Saminu Yusuf ne ya bayyana faruwar lamarin a wani sako da ya raba wa manema labarai.

Ya ce an samu gobarar ce a wani gidan mai da ake sayar da iskar gas da ke unguwar ‘Yankaba, kan titin zuwa Hadejia a Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar.

Yusuf, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1.14 na daren ranar Laraba, wadda ta shafi wani bangare na Gidan da kawunan da ke bayar da mai da wasu fitilu da ke gidan man.

“Mun amsa kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 1.14 na dare daga Malam Jibril Haruna da ke ofishin ‘yan sanda na unguwar Dakata.

“Muna samun wannan kira nan take muka tura tawagar jami’anmu na kar takwana suka kuma isa wurin da misalin karfe 1.22 na dare.

“An kubutar da wani matashi mai suna, Usman Muktar, dan shekara 18 daga cikin gobarar sai dai ya samu raunika a jikinsa,” in ji shi.

Jami’in hulda da Jama’a na hukumar yace, matashin da abun ya rutsa da shi, an yi nasarar tseratar da shi da ransa nan take kuma aka garzaya da shi babban Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano don kulawa da lafiyarsa.

Kazalika, Yusuf ya ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musababbin tashin gobarar.