✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta yi kisa a sansanin ’yan gudun hijira a Maiduguri

Ana zargin dai wutar ta tashi ne daga wani wajen da wani yake girki a sansanin.

Akalla mutum daya ya rasa ransa, wasu da dama kuma sun jikkata bayan wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Kalari Muna Elbadawy da ke birnin Maiduguri a Jihar Borno.

Aminiya ta gano cewa gobarar, wacce ta tashi da wajen misalin karfe 1:30 na daren Juma’a ta kuma lalata kayayyaki da dakunan ’yan gudun hijirar da dama.

Ana zargin dai wutar ta tashi ne daga wani wajen da wani yake girki a cikin sansanin.

Jami’in yada labarai na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a Jihar, Abdulkadir Ibrahim, ya tabbatar da faruwar gobarar.

Sai dai ya ce jami’ansu sun yi namijin kokari wajen ganin sun kashe ta ba tare da ta yi mummunar barna ba.

Ya ce jami’an hukumar tasu da na takwararta ta Jihar Borno (BOMESA) da kungiyar bayar da agaji ta Red Cross da sauran ma’aikatan agaji sun kai daukin gaggawa ga wadanda iftila’in ya shafa.