✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi barna a Cibiyar Binciken Cutar Kuturta mafi girma a Afirka

A ranar Litinin da ta gabata ce da misalin karfe 1200 na rana, wata mummunar gobara ta lashe katafaren dakin bincike da gwaje-gwajen cututtukan tarin…

A ranar Litinin da ta gabata ce da misalin karfe 1200 na rana, wata mummunar gobara ta lashe katafaren dakin bincike da gwaje-gwajen cututtukan tarin fuka da kuturta, da ke harabar katafaren Asibitin Kutare da Tarin Fuka da ke Saye, Zariya a Jihar Kaduna.

Aminiya a ziyarci asibitin inda ta ga irin barnar da gobarar ta yi kuma wakilinmu ya tattauna da wadansu daga cikin wadanda aka yi aikin kashe gobarar da su, da kuma wadansu daga cikin ma’aikatan asibitin wadanda ba su so a ambaci sunayensu ba.

Wadansu daga cikinsu sun cewa ana jin wata na’ura ce daga cikin na’urorin da ke dakin binciken ta kama da wuta, inda daga nan aka yi kokarin kashewa amma hakan bai yiwu ba sai da motocin kashe gobara na Gwamnatin Jihar Kaduna da taimakon motocin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya suka kawo dauki.

 Gobarar, wadda ta dauki tsawon awa biyar tana ci, majiyar tamu ta ce shi dakin binciken da ya kama da wuta ya kone kurmus. dakin binciken da ake kira da Ingilishi National Tuberculosis and Leprosy Centre an ce babu kamarsa a Nahiyar Afirka. Kuma yana daya daga cikin manyan dakunan bincike da gwaje-gwajen cutar tarin fuka da kuturta a duniya.

“Irin yadda wannan cibiya ta kone a gaskiya ba karamar asara aka yi ba, domin wuri ne da ake turo majinyata daga kasashe makwabta da kuma jihohin kasar nan. Don haka konewar da dakin ya yi zai sanya marasa lafiya masu yawa a cikin wahala, domin ba ko’ina ake da cibiyar gwaji irin ta wannan asibitin ba,” inji wani ma’aikacin cibiyar.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Shugaban Cibiyar, Dokta Labaran Shehu, inda ya ki cewa uffan, inda cikin fushi ya ce da wakilinmu, ai ba dole ne ya yi magana da shi ba. Kuma ya gargadi ma’aikatansa a gaban wakilinmu cewa kada kowa ya yi magana da ’yan jarida ko a bayan idonsa.

Binciken Aminiya ya gano, gobarar ta lashe na’u’rorin binciken cutar tarin fuka da kuturta na miliyoyin Naira da ba a tantance adadinsu ba.