Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ta ce ta samu rahoton mutuwar yara uku a wata gobara da ta tashi a garin Nguru na jihar.
Yayin da aka shiga yanayin sanyi, hukumar ta gargadi jama’ar jihar da yin taka tsan-tsan wajen amfani da wuta, da sauran na’urorin lantarki.
- Wayar salula ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89 a Ukraine
- Zan kayar da Zulum cikin sauki —’Yar takarar gwamna
“SEMA na son yin amfani da wannan kafa wajen yin kira ga shugabannin al’umma da magidanta da su yi taka-tsan-tsan a wannan lokaci, ta hanyar tabbatar da cewa an kashe duk na’urorin lantarki idan ba a amfani da su ba, a kashe itacen wuta yadda ya kamata bayan an kammala amfani da su.”
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa ta shafinta na Facebook ranar Alhamis.
SEMA ta kuma bayyana cewa ta samu rahoton afkuwar gobara a kananan hukumomin Damaturu da Fune a tsakanin ranakun 28, 30 ga Disamba, 2022 da kuma 4 ga Janairu, 2023.
Binciken da SEMA ta gudanar ya nuna yadda aka yi asarar dukiya kama daga kan gidaje, kayan abinci da sauransu.
Hukumar ta ce tana kokarin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa don rage musu radadin halin da suke ciki.