Wasu mutum hudu ’yan uwan juna sun mutu a wani ibtila’in gobara da ya auku a gidansu da ke garin Bida na Jihar Neja.
Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sun hada da wasu matan aure biyu na wani mai suna Sallau Kabaraini, sai kuma jikoki biyu na mamallakin gidan, Ahamadu Kabaraini wanda aka ruwaito ya dade da barin duniya.
- An fara yi wa fursunoni rigakafin cutar Coronavirus
- Sarkin Kano ya umarci jama’a su karbi allurar rigakafin coronavirus
- An gurfanar da matashi kan satar kayan wayar hannu na N1m
Mazauna tsohon garin na Bida sun tsinci kansu cikin jimami na wannan mummunan rashi da ya auku a ranar Litinin.
Baya ga salwantar rayukan mutanen hudu, babu wata dukiya da za a ci moriya a gidan da gobarar ta auku a yayin da dukkanin kayayyakin da ke cikinsa sun kone kurmus.
Mutanen da musibar ta ritsa da su kamar yadda Aminiya ta samu sun hada da Hajiya Salamatu da Hajiya Jummai, wadanda su ne matan Sallau, sai kuma jikokin marigayi Ahamadu, Hauwa da Khairatu.
A yayin da ba a iya gano musababbin tashin gobarar, sai ana zargin ba za ta rasa nasaba da wata matsala ta wutar lantarki da aka samu a gidan ba.
Tuni da Shugaban Sarakunan Gargajiya na Kasar Nufawa wato Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya aike da sakon ta’aziyya ga ’yan uwan wadanda wannan musiba ta shafa, inda ya nemi su jingina lamarin a matsayin kaddara daga Buwayi Gagara Misali.
Babban limamin garin Bida, Sheikh Adamu Yakatun ne ya jagoranci sallar jana’iza a kan mamatan kuma an binne su a bisa tanadin addinin Islama.