Gobara ta yi ajalin wani matashin malamin Musulunci mai shekara 29 a Jihar Jigawa.
Malamin mai suna Muhammad Ahmad, mazaunin kauyen Kuka ne da ke Karamar Hukumar Kirikasamma ta Jihar.
- Gumsu Abacha: Gwamnan Yobe ya ba da sadakin zinare 24
- Direbobi suna yajin aiki saboda ’yan bindiga a Zamfara
Jami’in yada labarai na Karamar Hukumar Kirikasamma, Sanusi Soro ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce wutar ta tashi ne a ranar Litinin da misalin karfe 2:00 na dare, inda ta hallaka Malam Muhammad tare da jikkata wasu almajirai biyu.