Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Kano, sun nuna cewar wuta ta kama a tashar raba wutar lantarki da ke Kofar Ɗan Agundi a jihar.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’ummar Musulmi a jihar, ke dakon ganin jinjirin watan azumin Ramadan.
Aminiya ta gano yadda gobarar ta kone manyan injina da taransufoma masu yawa.
A cewar wani jami’in gudanarwa na Kamfanin Raba Wutar Lantarki a Kano (TCN), gobarar ta ƙone manyan taransufoma biyu masu raba wutar lantarki a jihar.
“Ni ma ba na ofis amma sai aka sanar da ni cewa taransufoma biyu sun ƙone, amma akwai guda ɗaya tana aiki, akwai wata sabuwa wadda har yanzu ba a fara aiki da ita ba.”
Kazalika, jami’in ya ce tashin gobarar ba zai hana samun wutar ba.
“Wutar ba za ta hana raba wutar lantarki ba tunda guda ɗaya tana aiki. Amma komai zai daidaita yadda ake so da zarar an gyara abubuwan da suka ƙone.”
Mutanen yankin sun bayyana cewar ba su san musabbabin tashin wutar ba.
Jin ta bakin kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.