✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a tashar iskar gas a Legas

Rahotanni da muka samu sun ce an samu fashewar gas da sanyin asubahin Alhamis a Jihar Legas. Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto wutar da ta…

Rahotanni da muka samu sun ce an samu fashewar gas da sanyin asubahin Alhamis a Jihar Legas.

Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto wutar da ta tashi na kara ci a tashar iskar gas din da abin ya auku a Karamar Hukumar Alimosho.

Mazauna a unguwar Baruwa da lamarin ya faru na ta guje-guje domin tsira da rayuwarsu.

Hukumar ba da agaji ta jihar Legas (LASEMA) ta je lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:45 na asuba wanda nan take bayan aukuwar iftila’in da fara aikin ceto.

Gobarar gas din ta ranar Alhamis na zuwa ne mako uku bayan makamanciyarta ta raunata mutum 30 tare da kona gine-gine 23 a jihar ta Legas.