Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce gobara ta kama tare da lalata wani sashe na Makarantar Firamaren Ma’aikatan Jami’ar Bayero ta Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba a Kano.
- Rasha za ta ci gaba da katse wa kasashen Turai iskar gas —Putin
- Mutum 189 sun kamu da Kwalara a kananan hukumomi 20 a Kano
Ya ce gobarar ta tashi a makarantar ce da yammacin ranar Talata.
A cewar Abdullahi, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 05:53 na yamma daga wani Halliru Bello, inda nan take muka aike da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 5:58 na yamma domin hana gobarar ta yadu zuwa wasu sassa na makarantar.
“Wani gini mai tsayi kafa 200 mai dauke da ofishin Shugaban Makarantar Firamaren da ofishin malamai maza da ofishin malamai mata da dakin ajiya da kuma bandaki sun kone a sanadin tashin gobarar.
“Ana binciken musabbabin tashin gobarar,” in ji shi.