An wayi garin ranar Litinin da gobara a Kasuwar Singer, wadda ta shahara wajen sayar da kayan abinci a Jihar Kano.
Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne a cikin tsakar dare kuma har zuwa wayewar garin Litinin ba a gana shawo kan wutar ba.
- NAJERIYA A YAU: Ko Yaya Mulkin Tinubu Zai Kasance?
- Zulum ya kai wa iyalan masuntan da ISWAP ta kashe tallafi
“Har yanzu wutar tana nan tana ci. duk daga daren juya (Lahadi); jami’an kashe kogara na kirarin kashewa, amma dai har yanzu wutar na ci gaba da ci a wannan kasuwa,” in ji wani ganau, Mubarak Sani Muhammad.
Wani jami’in da ya nemi a boye sunansa, saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance ya ce, “Da misalin karfe 2 na dare muna cikin aiki muka samu rahoton gobara ta tashi a Kasuwar Singer.”
Wannan gobara na zuwa ne kwanaki kadan bayan gobarar kasuwannin Rimi da kuma Kurmi masu tazarce ’yan kilomitoci daga Kasuwar Singer.
Mubarak,wanda ya yada bidiyon yadda ake aikin kashe gobarar kai-tsaye ta Facebook, ya bayyana cewa jami’an kashe gobara na kokarin shawo kan wutar da take ci gaba da barna a sassan kasuwar ta Singer.
An ga yadda wasu daga cikin ’yan kasuwar kokarin kwashe abin da za su iya na dukiyarsu da ya rage a Kasuwar Singer.
“Ya kamata jami’an kashe gobara su kawo dauki domin wutar na ci gaba da ruruwa daga bangarori daban-daban.”