Gobara ta cinye dukukiyo masu yawan gaske a wata kasuwar doya da ke Jihar Filato.
Kayan abinci da sauran kadarori na miliyon Naira sun kone kurmus a gobarar a Babbar Kasuwar Doya ta Namu da ke Karamar Hukumar Qua’anpan ta Jihar.
- Ta kashe jaririyarta, ta jefa gawar a kogi
- ‘Yadda na gudu a hannun masu garkuwar da suka kama mu’
- An sauya tsarin Sallar Tarawih da Tahajjud a Masallacin Harami —Sudais
- Taron Tinubu: An tsaurara tsaro a Gidan Gwamantin Kano
Majiyarmu ta gano cewa an yi gobarar ce a ranar Lahadi, inda kawo yanzu manoma dan sauran ’yan kasuwar ke jujayin irin asarar da suka yi sakamakonta.
Wadanda suka yi asarar sun roki gwamnati da kawo musu dauki domin su samu su farfado da jarinsu bayan asarar da suka yi a gobarar, domin ci gaba da samar da kayan abinci.
’Yar Majalisar Dattawa mai wakiltar Filato ta Kudu, Farfesa Nora Dadu’ut ta jajanta wa ’yan kasuwar da sauran wadanda abin ya shafa tare da yi musu addu’ar samun farfadowa.
Ita ma ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin jin kai da su taimaka wa ’yan kasuwar domin su samu su farfado da wuri daga iftila’in da ya same su.