Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai a Kwalejin Kimiyya ta Alhaji Musa Muhammad Kigera da ke Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Shugaban Kwalejin, Ibrahim Mohammed Kontogora, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho, sai dai ya ce ba a samu asarar rai ba.
- ’Yan casu muka kama ba masu hada auren jinsi ba —Hisbah
- Mun dauki matakan kawo karshen karancin mai —NNPC
“Gaba daya dakin kwanan dalibai na ‘Red House’ ya kone dauke da kayayyakin dalibai, amma ba a samu asarar rai ba,” a cewarsa.
Shugaban makarantar ya kara da cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 1 na dare a yayin da dalibai ke barci, kafin daga bisani jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Neja su je su kashe ta.
Ya kuma bayyana cewa ana gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa tashin gobarar, ko da yake ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa.