✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a barikin sojoji a Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta kashe gobarar aka yi a Barikin Sojoji na Bukavu a Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar da kashe wata gobara da ta tashi a ofisoshi 11 da ke barikin sojoji na Bukavu a Kano.

Mai magana da yawun Hukumar, Saminu Yusuf ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Juma’a.

“Bayan samun rahoton abin da ke faruwa, nan take muka aike da jami’anmu da misalin karfe 9:19 na dare don su kashe wutar.

“An yi nasarar kashe gobarar ba tare da an samu salwantar rayuka ba,” a cewarsa.

Ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 9:10 na daren ranar Alhamis, kuma ta kone dakin ajiye abinci da bandakuna.

Bayan gano abin da ya asassa gobarar, ya shawarci mutane da suke ajiye kurtun kashe wuta a gidaje da ofisoshi don kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.